Tuesday, October 19, 2010

kanun labarai

Za a zabtare kudaden da ake kashewa sojojin Burtaniya

David Cameron
David Cameron ya gabatar da jawabin ne a gaban majalisar kasar
Pira ministan Burtaniya, David Cameron, ya bayyana shiri mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu, na rage yawan kudaden da kasar ke kashewa ta fuskar tsaro.
A karkashin shirin, sojoji dubu bakwai na rundunar mayakan kasa za su rasa aikinsu.
Hakanan kuma za a rage sojoji dubu biyar-biyar daga rundunonin mayakan ruwa da na sama.
Sai dai duk da haka, in ji Mista Cameron din, Burtaniya za ta fi zama cikin kyakkyawan shirin tinkarar barazanar da ba a saba gani ba.
Wannan dai shi ne zabtare kudaden da ma'aikatar tsaro ke kashewa mafi girma tun karshen yakin cacar baki.

'kwamacalar jam'iyyar Labour'

David Cameron ya bayyana zabge gurabun ayyukan fararen hula dubu 25 a ma'aikatar ta tsaro, tare kuma da rage girman sojin Burtaniya da dubu 7.
Haka kuma ya bayyana gagarumin ragi a jiragen sama ga rundunar sojin sama da kuma jiragen ruwa na sojin ruwa.
Mr Cameron ya hakkake cewar sauye-sauyen ga dakarun na Burtaniya, sun biyo bayan damuwar da ake da ita ga sha'anin tsaro ne ba don rage kudaden da suke kashewa ba.
To amma ya zargi gwamnatin Jama'iyar Labour da ta gabata da laifin barin irin wannan kwamacala, tare da kashe kasafin kudin tsaro fiye da kima da dola biliyan 60.
Ya gayawa kakakin majalisar kasar cewa wannan ma wani bangare ne na inda Gwamnatin da ta gabata ta yi kuskure matuka.
Sai dai Shugaban Jama'iyar Labour Ed Milliband, ya bayyana sake nazartar kudin da ake kashewa a bangaren na tsaro da cewar wani cikakken holoko ne.

No comments:

Post a Comment